Sakaci ko Hadin baki Sace ‘Yan Matan Sakandiren Dapchi?

 

Daga Aliyu Muhammad, Kaduna

Gamaiyar kungiyoyin matasan Arewa a taraiyar najeriya sun nuna rashin jin dadin su da sakaci da aka samu har ‘yan kungiyar ta’adda ta boko haram suka sake sace ‘yan mata sama da Dari da goma a sakandiren yan mata da take a garin Dapchi ta jahar yobe.

Nastura Ashir Sharif shine wanda Yashaidawa manema labarai cewa gaskiya wannan batu na satar wadannan yara sakacine kokuma hadin baki domin babu yadda za’ace a kwashe sama da awa uku ana diban wadannan yara ace babu wasu jami’an tsaro da suka Kawo dauki.

Gamaiyar kungiyoyin matasan Arewan sun shawarci shugaba muhammadu buhari da yasa kaimi ga hukumomin tsaro domin dawo da yaran sakandiren Dapchi domin sadasu da iyayensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *