Za’ayi Asarar rayuka middin ba’a soke zaben jahar zamfara ba~~gamaiyar jam’iyun Adawa:

Daga Hussaini Baba gusau
Jam’iyun adawa da ke cikin jahar Zamfara, sun tabbatar da cewa ‘ idan hukumar zabe ta kasa INEC  bata rushe zaben da ya gudana a makwan da ya wuce na Shugaban kasa da na ‘yan majalissun tarayya ba da ke cike da magudi lalllai za’a zubar da jini
Kuma za’a rasa rayuka masu dinbin yawa.
Shugaban hadakar jam’iyun kuma dan takarar gwamna a jam’iyar Apga Alhaji Sani Abdullahi Wanban Shinkafi  ne ya tabbatar da haka a dakin taron wakilan
 kafafen yada labarai da ke fadama a gusau Babban birnin jahar Zamfara.
 Shugaban hadakar ya bayyana cewa suna da tabbaci, tun a ranar jajibirin zaben ne a ka shirya wannan makircin na yin mugun magudi a hedkwatar ‘yan sanda da ke jahar.
yace an shirya magudin ne tare da Kwamishinan ‘yansanda  Celestine Okoye da Kwamishiniyar zabe ta jahar Dakta Asama’u mai Kudi da Shugaban jam’iyar APC na jahar Zamfara,Honarabul Lauwali gamdon kaura da Sakataren sa Honarabul Sani Mono.
Ya kara da cewa na je hedkwatar a lokacin da suke shirya wannan badakala domin kai kokena amma aka hanani Shiga domin sun san  makircin da su ke kullawa.
shugaban hadakar jam’iyun yace don haka sai na nemi ganin kwamishina domin jin ba’asin hanani shiga sai ya turomani mataimakinsa akan in fada masa abunda ke tafe dani, ni kuma na tsaya kai da fata nace shi na ke san gani kuma nayi nasara ya fito ya saurareni kuma  na tabbatar masa da cewa ” bamu yarda da canza kayan zabe ba da Kwamishiniyar ke sanyi nan dai na fada masa korafin mu amma babu wani mataki da ya dauka.
Dan takarar yacigaba da cewa  an saci akwatina a wasu runfunan zaben, kuma anyi amfani da mazabun ‘yan gudun hijira domin basu kudi  naira dari biyar wasu kuma  dubu daya dan a zabi ‘yan takarar karkarun gwamnati gwamnati, kuma yace an kama mutane dumu -dumu sun kulle kansu a daki suna dangwalen kuri’u kuma babu matakin da hukumar zabe da kuma jami’an tsaro suka dauka dimin hana hakan.
sai yace wannan ya tabbatar da cewa kitsa wannan makircin akayi, don haka mu jam’iyun adawa bazamu lamunci wannan ta’addancin ba.
A kan haka mu ke kira ga Sufeto janar na ‘yansanda ya gaggauta kauda Kwamishinan sa daga jihar Zamfara.
 ita kuma hukumar zabe mai zaman kata ta qasa INEC  tayi gaggawar dakatar da Kwamishiniyar zaben jihar domin bata cancanci yin wannan aikin ba.
Daga karshe wanban Shinkafin yace shi a madadin sa na shugaban jam’iyun adawa sun dau alwashin bin umarnin da Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bada na ganin bayan duk wanda ya saci akwatin zabe ko ya naimi kawo magudin zabe a jihar Zamfara, a zaben gwamnoni mai zuwa da na ‘yan majalisun jiha.
Gamaiyar jam’iyun sun hada da jam’iyar PDP, Apga ,NRM ,ADC ,YPP ,Accord ,ABP , da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: