Sheik zakzaky da matarsa sun isa kasar India:

Babban malamin addinin musulunci a Najeriya sheik Ibrahim zakzaky da matarsa malama zeenatu sun isa babban Asibitin kasar India domin neman lafiya, malamin da matarsa dai sun dauki tsawon lokaci a hannun jami’an farin Kaya na DSS, daliban malamin dai a Najeriya da sauran kasashen duniya sunyita yin zanga zangar lumana domin a Saki malamin nasu hakan kuma ya jawo asarar rayukan daliban malamin a Najeriya.

Daliban malamin dai sun zargi gwamnatin shugaba Buhari da kawo tarnakin game da sakin malamin nasu da dan Kanzaginsa gwamnan jahar kaduna malam Nasiru el rufa’i, Inji mabiyan malamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: