Matan kananan hukumomi 23 na  jahar Kaduna sun samu horo a gonar teku:

Matan kananan hukumomi 23 na  jahar Kaduna sun samu horo a gonar teku:

Daga Aliyu muhammad, kaduna
Kungiyar sasanta tsakanin Addinai ta Interfaith ta horar da mata daga kananan hukumomi 23 da suke a jahar kaduna yadda zasu koyi dashen itatuwa da kiwan kifi, domin dogaro da kansu da kuma yadda za’a kaucewa kwararowar hamada.
Wacce tayi jawabi a madadin kungiyar Hajiya Ramatu Adamu tace sun kawo wannan horo ne gonar teku domin itace kadai  gona a kaduna wacce take horar da matasa yadda zasu koyi dashen itatuwa da kiwan kifi a jahar ta kaduna.
Hajiya Ramatu tayi kira ga gwamnati da tayi kokari domin tura matasa koyon dashen itace  da kiwan kifi a gonar ta teku.
Alhaji Ibrahim salisu mai teku shine shugaban gonar ta teku kuma yayi kira ga kungiyoyi da suyi koyi da kungiyar ta Interfaith domin koyawa matasa sana’a.
Daga karshe Ibrahim salisu yayi kira ga Al’umma  da su kaucewa sare itatuwa domin hakan yana da illa ga rayuwar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: