Wasu da ake zargin Mahara ne sun kashe Sojoji Tara a Zamfara: 

Daga Hussaini Ibrahim,  Gusau
Wasu da ake zargin Mahara ne a kauyan Sanke da ke karamar hukumar Anka cikin jihar Zamfara , sunyiwa sansanin Sojoji kwantan bauna inda suka kashe Sojoji tara ,a ranar alhamis da  ta gabata.
 Wannan harin ya biyo bayan wani rahoto ne na siri da gwamnatin  ta  ban kado, rahotan ya nuna cewa wasu suna nan suna  kokarin gayyato ‘yan Boko haram damin su kaddamar da hare hare a wasu kananan hukumomi bakwai ciki  har da karamar hukumar Anka da akayiwa Sojonin kwantan bauna.
Wata da take da ruwa da tsaki a cikin   gwamnatin ta jahar kuma ta  nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa wadan nan mahara ramuwar gayya ne suka mai da a sakamakon yadda sansanin Sojojin suke yiwa maharan  dauki dai dai duk da sulhun da akayi da su da gwamnatin jihar ta  Zamfara, su dai  sojojin basu bar maharan haka nan ba.
 Kuma a ranar laraba ne sansanin maharan suyi ayari suka shiga dazukan karamar hukumar Anka inda suka yada zango a Mayanci suka kwashe kayan yakin  jama’a suka kara guziri.
 Manaima labarai sunta kokarin jin ta bakin, kakakin Rundunar Hadarin Daji,  Kaftin Oni Or isan , amma abin  yaci tura .yace zai tuntubi manaima labaran, zuwa wani lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: